Acts 13:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani mutumin Yahuda mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu,
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ سُنْ ظَظْذَاغَ ڟِبِرِنْ دُكَ حَرْ بَڢُواسْ، سُكَ سَدُ دَ وَنِ بَيَهُودٜىٰ مَيْ سِحِرِ، شِ أَنَّبِنْ ڧَضْيَا نٜىٰ، مَيْ سُونَ بَرْ يُواْشُوَ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan sun zazzaga tsibirin duka har Bafusa, suka iske wani mai sihiri, annabin ƙarya, Bayahude, mai suna Bar-yashu'a,