Acts 14:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A Listira kuwa akwai wani gurgu zaune a ƙafafunsa, wanda gurgu ne tun haihuwa, kuma bai taɓa tafiya ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَ لِسْتِرَ كُوَ أَݣَويْ وَنِ مُتُمْ وَنْدَ شِ غُرْغُ نٜىٰ، بَيْتَٻَيِنْ تَڢِيَ بَ تُنْدَ عَكَ حَيْڢٜىٰشِ؞ يَنَ ظَوْنٜىٰ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, a Listira akwai wani mutum a zaune, wanda ƙafafunsa ba su da ƙarfi, gurgu ne tun da aka haife shi, bai ma taɓa tafiya ba.