Acts 15:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai waɗansu daga cikin masu bin da suke na ƙungiyar Farisiyawa suka miƙe tsaye suka ce, “Dole ne a yi wa Al’ummai kaciya a kuma bukace su su yi biyayya da dokokin Musa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا وَطَنْسُ مَاسُبِے، یَنْ ڧُنْ‌غِيَرْ ڢَرِسِيَاوَا، سُكَتَاشِ ڟَيٜىٰ سُكَثٜىٰ «دُواْلٜىٰنٜىٰ عَيِ وَمَاسُبِے وَطَنْدَ بَا يَهُودَاوَا بَ كَاثِيَ، عَكُمَسَاسُ دُواْلٜىٰ سُبِے كُواْيَرْوَرْ مُوسَٰى؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma waɗansu masu ba da gaskiya, 'yan ɗariƙar Farisiyawa, suka miƙe, suka ce, “Wajibi ne a yi musu kaciya, a kuma umarce su, su bi Shari'ar Musa.”