Acts 15:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan aka yi muhawwara da sosai, sai Bitrus ya miƙe tsaye ya yi musu jawabi ya ce, “’Yan’uwa, kun san cewa a kwanakin baya Allah ya yi zaɓe a cikinku don Al’ummai su ji daga leɓunana saƙon bishara su kuma gaskata.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْدَ عَكَيِ تَ غَرْدَمَ سُواْسَيْ، سَيْ بِتْرُسْ يَتَاشِ ڟَيٜىٰ يَثٜىٰ مُسُ «یَنْعُوَ، كُنْ سَنِ تُنْ تُنِ اللَّهْ يَذَاٻٜىٰنِ عَثِكِنْكُ، ثٜىٰوَ تَوُرِينَ نٜىٰ وَطَنْدَ بَا يَهُودَاوَا بَ ذَاسُجِ لَابَرِ مَيْ دَاطِے، سُكُمَ بَادَ غَسْكِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan an yi ta muhawwara da gaske, Bitrus ya miƙe, ya ce musu, “Ya 'yan'uwa, kun sani tun farkon al'amari, Allah ya yi zaɓe a cikinku, cewa dai ta bakina ne al'ummai za su ji maganar bishara, su ba da gaskiya.