Acts 16:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba zato ba tsammani sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa har tushen ginin kurkukun ya jijjiga. Nan da nan sai duk ƙofofin kurkukun suka bubbuɗe, sarƙoƙin kowa kuma suka ɓaɓɓalle.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَا لَابَرِ سَيْ عَكَيِ وَتَ بَبَّرْ ضَوَرْ ڧَسَا، حَرْ تُوشٜىٰنْ غِنِنْ كُرْكُكُنْ يَغِرْغِظَ؞ نَنْ دَ نَنْ ڧُواْڢُواْڢِنْ دُكَ سُكَ بُوطٜىٰ، سَرْڧُواْڧِنْ دُكَنْ یَنْ كُرْكُكُنْ سُكَ كُنْثٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
farat ɗaya, sai aka yi wata babbar rawar ƙasa, har harsashin ginin kurkuku ya raurawa. Nan da nan ƙofofin suka bubbuɗe, marin kowa kuma ya ɓalle.