Acts 17:34 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗansu mutane kima suka zama mabiyan Bulus suka kuwa gaskata. A cikinsu kuwa akwai Diyonasiyus ɗan Majalisar Areyofagus, haka kuma wata mace mai suna Damaris, da waɗansu dai haka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا وَطَنْسُنْسُ سُكَ كُواْمَ وَجٜىٰنْ بُلُسْ، سُكَ بَادَ غَسْكِيَ؞ عَثِكِنْسُ أَݣَويْ دِيُواْنِسِيُسْ، طَنْ مَجَلِسَ دَ وَتَ مَثٜىٰ مَيْ سُونَ دَمَرِسْ دَ وَطَنْسُ كُمَ تَرٜىٰدَسُو؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma waɗansu mutane suka koma wajensa suka ba da gaskiya, a cikinsu har da Diyonisiyas, ɗan majalisar Tudun Arasa, da wata mace mai suna Damarisa, da waɗansu dai haka.