Acts 18:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ana cikin haka sai wani mutumin Yahuda mai suna Afollos, ɗan ƙasar Alekzandariya, ya zo Afisa. Shi masani ne, yana da cikakken sani na Nassosi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَنَانً سَيْ وَنِ بَيَهُودٜىٰ مَيْ سُونَ أَڢُواْلُّواسْ يَذُواْ أَڢِسَ؞ شِے كُوَ طَنْ غَرِنْ إِسْكَنْدَارِيَا نٜىٰ، مَيْ عِيَ مَغَنَ، يَكُمَ سَنْ رُبُوتَثِّيَرْ مَغَنَرْ اللَّهْ سُواْسَيْ سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, wani Bayahude mai suna Afolos ya zo Afisa. Shi kuwa asalinsa mutumin Iskandariya ne, masani ne kuwa, ya san Littattafai ƙwarai da gaske.