Acts 19:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sana’an nan ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ تَاشِنْ حَنْكَلِ يَڢَارَ دَ وَنِ مَڧٜىٰرِ مَيْ سُونَ دِمِتِرِيُسْ وَنْدَ يَكٜىٰ أَمْڢَانِ دَ أَظُرْڢَا يَنَ ڧٜىٰرَ صِڢَّرْ هَيْكَلِنْ أَرْتٜىٰمِسْ؞ شِے دَ مَعَيْكَتَنْسَ سُنَ سَامُنْ كُطِ تَوَنَّنْ سَنَعَرْسُ بَكَطَنْبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin akwai wani maƙerin farfaru, mai suna Dimitiriyas, mai ƙera surorin haikalin Artimas da azurfa, ba kuwa ƙaramar riba yake jawo wa masu yin wannan sana'a ba.