Acts 19:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Akwai hatsari, ba kawai cewa sana’armu za tă rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a ko’ina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُواْ، أَݣَويْ حَڟَرِ ڢَا؞ ذَاعَ ٻَاتَ سُونَنْ عَيْكِنْمُ؞ بَنْدَ حَكَمَا، حَرْ دَ هَيْكَلِنْ بَبَّنْ أَلِّيَ أَرْتٜىٰمِسْ ذَاعَ مَيْدَشِ بَنْظَ، حَرْ كُمَ أَ رَبَ أَلِّيَرْ دَ دَرَجَرْتَ، عِتَ وَدَّ دُكْ ڧَسَرْ أَسِيَ، كَيْ، حَرْ مَا دُكَنْ دُونِيَا تَكٜىٰ بَوْتَا مَتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga shi kuma, akwai hatsari, ba wai cinikinmu kawai ne zai zama wulakantacce ba, har ma haikalin nan na uwargijiya Artimas mai girma zai zama ba a bakin kome ba, har kuma a raba ta da darajarta, ita da duk ƙasar Asiya, kai, har duniya ma duka suke bauta wa.”