Acts 2:29 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“’Yan’uwa, zan iya tabbatar muku gabagadi cewa kakanmu Dawuda ya mutu aka kuma binne shi, kabarinsa kuwa yana a nan har yă zuwa yau.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
یَنْعُوَنَ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا، ذَنْعِيَيِ مُكُ مَغَنَ بَابُ شَكَّ غَمٜىٰدَ كَكَنْمُ دَاوُدَ؞ دَاوُدَ يَمُتُ، أَنْبِنّٜىٰشِ، كَبَرِنْسَ كُمَ يأَنَانً تَرٜىٰدَمُو هَرْوَيَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya 'yan'uwa, na iya yi muku magana da amincewa a game da kakanmu Dawuda, cewa ya mutu, an binne shi, kabarinsa kuma yana nan gare mu har ya zuwa yau.