Acts 22:29 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗanda dā suke shirin yin masa tambayoyi suka ja da baya nan da nan. Shugaban ƙungiyar sojan kansa ya tsorata da ya fahimci cewa ya sa wa Bulus, ɗan ƙasar Roma sarƙa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ شِرِنْ بِنْثِكٜىٰنْسَ سُكَجَا بَايَ نَنْ دَنَنْ؞ شِمَا شُوغَبَنْدَ يَغَانٜىٰ بُلُسْ مَيْ یَنْثِنْ رُواْمَ نٜىٰ سَيْ يَجِڟُواْرُواْ، غَاشِ كُوَ يَارِغَا يَطَوْرٜىٰشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka, waɗanda suke shirin tuhumarsa, suka rabu da shi nan da nan. Shi ma shugaban da ya fahimci Bulus Barome ne, sai ya tsorata, ga shi kuwa, ya ɗaure shi.