Acts 22:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ni mutumin Yahuda ne haifaffen Tarshish na Silisiya, amma a nan birnin ne aka rene ni. Aka horar da ni sosai cikin dokokin kakanninmu a ƙarƙashin Gamaliyel ni ma dā mai himma ne cikin bauta wa Allah kamar yadda kowannenku yake a yau.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«نِے بَيَهُودٜىٰ نٜىٰ، أَنْحَيْڢٜىٰنِ أَ تَرْسُسْ، ڧَسَرْ كِلِكِيَ، عَمَّا أَنَنْ غَرِنْ نَيِ غِرْمَ؞ نَيِ مَكَرَنْتَ عَڧَرْڧَشِنْ غَمَلِيٜىٰلْ، وَنْدَ يَكُواْيَ مِنِ كُواْمٜىٰ غَمٜىٰدَ كُواْيَرْوَرْ كَاكَنِّنْمُ؞ إِنَدَ كِيشِنْ بَوْتَرْ اللَّهْ ، كَمَرْ يَدَّ دُكَنْكُ كُكٜىٰيِ عَيَوْ،
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ni bayahude ne, haifaffen Tarsus, ƙasar Kilikiya, amma a nan garin na girma, aka kuma karantar da ni wurin Gamaliyal, bisa ga tsarin tsanantacciyar hanyar nan ta Shari'ar kakanninmu. Ina mai himmar bauta wa Allah, kamar yadda dukanku kuke a yau,