Acts 22:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
kamar yadda babban firist da dukan Majalisa za su iya shaida. Na ma karɓi wasiƙu daga gare su zuwa ga ’yan’uwansu a Damaskus, na kuma tafi can don in kawo waɗannan mutane a daure zuwa Urushalima don a hukunta su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَبَّنْ ڢِرِسْتِ مَا دَ دُكَنْ مَجَلِسَرْ شُوغَبَنِّنْ جَمَعَ ذَاسُ عِيَ شَيْدَتَ؞ دَغَ وُرِنْسُ نٜىٰ نَكَرْٻِ وَسِيڧُ ذُوَاغَ یَنْعُوَنْمُ يَهُودَاوَا عَثِكِنْ دِمَشْڧُ؞ نَتَڢِے وُرِنْ دُواْمِنْ إِنْكَامَ مَاسُبِنْ حَنْيَرْ نَنْ وَطَنْدَ سُكٜىٰ عَثَنْ مَا، إِنْكَٰوُاْسُ عُرُوشَلِيمَ دُواْمِنْ أَ حُكُنْتَسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Babban firist ma da dukan majalisar shugabannin jama'a za su iya shaidata, daga gunsu ne kuma na karɓi wasiƙu zuwa ga 'yan'uwanmu Yahudawa, na tafi Dimashƙu, don in ɗebo waɗanda suke can ma, in zo da su Urushalima a ɗaure, a azabta su.”