Acts 23:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Bulus ya kira ɗaya daga cikin jarumawan ya ce, “Ka kai wannan saurayi wurin shugaban ƙungiyar soja; yana da wani abin da zai faɗa masa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بُلُسْ كُوَ يَكِرَا وَنِ بَبَّنْ سُواْجَنْ رُواْمَ يَثٜىٰ «كَكَيْ سَوْرَيِنَّنْ وُرِنْ شُوغَبَا، يَنَدَ وَتَ مَغَنَرْ دَ ذَيْ غَيَ مَسَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bulus kuwa ya kira wani jarumi ya ce, “Ka kai saurayin nan wurin shugaba, yana da wata magana da zai faɗa masa.”