Acts 24:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan kwana biyar sai Ananiyas babban firist ya tafi Kaisariya tare da waɗansu daga cikin dattawa da kuma wani lauya mai suna Tertullus, suka kawo ƙararsu game da Bulus a gaban gwamna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ ݣُونَ بِيَرْ سَيْ بَبَّنْ ڢِرِسْتِ، هَنَنِيَ، يَذُواْ تَرٜىٰدَ وَطَنْسُ شُوغَبَنِّ دَ كُمَ وَنِ لَوْيَ مَيْ سُونَ تَرْتُلُسْ، دُواْمِنْ سُيِ ڧَارَرْ بُلُسْ أَغَبَنْ ڠُومْنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan kwana biyar sai babban firist, Hananiya, ya zo tare da waɗansu shugabanni, da kuma wani lauya, mai suna Tartulus, suka yi ƙarar Bulus a gaban mai mulki.