Acts 25:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In kuwa ina da wani laifin da ya isa kisa, ban ƙi in mutu ba. Amma in ƙarar da waɗannan Yahudawa suka kawo a kaina ba gaskiya ba ne, ba wanda yake da iko ya ba da ni a gare su. Na ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ نِے مَيْ لَيْڢِے نٜىٰ، حَرْ نَيِ لَيْڢِنْدَ يَ إِسَ عَكَشٜىٰنِ، أَيْ، بَذَنْڧِ عَكَشٜىٰنِبَ؞ عَمَّا عِدَنْ بَا وَتَ غَسْكِيَ عَثِكِنْ ڧَارَرْ دَسُكٜىٰيِ، تُواْ، بَا مَيْ عِيَ بَادَنِ غَرٜىٰسُ؞ نَا ضُواْڧَا أَطَوْكَكَ ڧَارَتَ ذُوَا غَبَنْ كَيْسَرْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, in ni mai laifi ne, har na aikata abin da ya isa kisa, ai, ba zan guji a kashe ni ba, amma in ba wata gaskiya a cikin ƙarata da suke yi, to, ba mai iya bashe ni gare su don a faranta musu rai. Na nema a ɗaukaka ƙarata gaban Kaisar.”