Acts 25:23 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kashegari Agiriffa da Bernis suka yi shiga irin ta sarauta suka shiga ɗakin jama’a tare da manyan sojoji da manyan mutanen birni. Da umarnin Festus, sai aka shigo da Bulus.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُواْ، وَشٜىٰغَرِ سَيْ أَغِرِڢَّ دَ بَنِسْ سُكَ شِغُواْ دَ دَرَجَ إِرِنْ تَسَرَاكُنَ، سُنْذُواْ تَرٜىٰدَ شُوغَبَنِّنْ يَاڧِ دَ كُمَ مَنْيَنْ غَرِنْ؞ سَيْ ڢٜىٰسْتُسْ يَبَادَ عُمَرْنِ أَ شِغُواْ دَ بُلُسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, kashegari sai Agaribas da Barniki suka zo a cikin alfarma, suka shiga ɗakin majalisa tare da shugabannin yaƙi da kuma jigajigan garin. Sai aka shigo da Bulus da umarnin Festas.