Acts 25:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Festus ya ce, “Sarki Agiriffa, da kuma dukan waɗanda suke tare da mu, kun ga wannan mutum! Dukan jama’ar Yahudawa sun kawo mini kararsa a Urushalima da kuma a nan Kaisariya, suna kururuwa suna cewa bai kamata a bar shi da rai ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ ڢٜىٰسْتُسْ يَثٜىٰ «سَرْكِے أَغِرِڢَّ دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ نَنْ تَرٜىٰدَمُو، غَا مُتُمِنْ دَ دُكْ جَمَعَرْ يَهُودَاوَا سُكَ كَٰوُاْ مِنِ ڧَارَرْسَ أَ عُرُوشَلِيمَ دَ كُمَ أَنَنْ، حَرْ سُنَ إِيهُ وَيْ بَيْكَمَتَ عَبَرْشِ دَ رَيْبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Festas ya ce, “Ya sarki Agaribas, da dukan mutanen da suke tare da mu, kun ga mutumin nan da duk jama'ar Yahudawa suka kawo mini ƙararsa a Urushalima, da kuma nan, suna ihu, bai kamata a bar shi da rai ba.