Acts 25:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ba ni da wata tabbatacciyar maganar da zan rubuta wa Mai Girma game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku duka, musamman a gabanka, Sarki Agiriffa, saboda a sakamakon wannan bincike zan iya samun abin da zan rubuta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا بَانِ دَ وَتَ تَبَّتَاثِّيَرْ مَغَنَرْ دَ ذَنْ رُبُوتَ وَمَيْغِرْمَ سَرْكِنْ رُواْمَ عَكَنْسَ؞ سَبُواْدَ حَكَ نَكَٰوُاْشِ غَبَنْكُ، مُسَمَّنْ غَبَنْكَ، سَرْكِے أَغِرِڢَّ، دُواْمِنْ بَايَنْدَ مُكَ بِنْثِكٜىٰشِ، كُواْ ذَنْسَامِ أَبِنْدَ ذَنْ رُبُوتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ba ni da wata tabbatacciyar magana da zan rubuta wa ubangijina game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku, musamman kuwa a gabanka, ya sarki Agaribas, don bayan an yi bincike, ko na abin da zan rubuta.