Acts 27:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da yake tashar jirgin ruwan ba tă dace a ci damina a can ba, yawanci suka ba yanke shawara cewa mu ci gaba da tafiya, da bege za mu kai Funis mu ci damina a can. Wannan tashar jirgin ruwa ne a Kirit, tana fuskantar kudu maso yamma da kuma arewa maso yamma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَيَكٜىٰ مَڢَكَرْ لَسِيَ بَيْيِݣَوْ جِضَاغٜىٰ سُثِ دَامِنَ أَنَنْبَ، سَيْ يَوَنْثِنْسُ سُكَ يَرْدَ عَثِيغَبَدَ تَڢِيَ، عَكُمَيِ ڧُواْڧَرِ عَكَيْ ڢِنِكسْ، إِنْ يَيِوُ، دُواْمِنْ سُثِ دَامِنَ عَثَنْ؞ ڢِنِكسْ كُوَ وَتَ تَشَرْ جِضْغِ ثٜىٰ عَڟِبِرِنْ كِرِتْ وَدَّ تَكٜىٰ ڢُسْكَنْتَرْ أَرٜىٰوَ تَوَجٜىٰنْ يَمَّ دَ كُمَ كُدُ تَوَجٜىٰنْ يَمَّ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da yake mafakar nan ba ta kamaci jirage su ci damuna a ciki ba, sai yawanci suka kawo shawara a tashi daga nan, ko ta ƙaƙa su iya kaiwa Finikiya, wata mafakar tsibirin Karita, mai duban gabas maso arewa da kuma gabas maso kudu, su ci damuna a can.