Acts 27:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tafiyar ta ɗauki kwanaki da yawa muna yi kaɗan-kaɗan da ƙyar muka iso kusa da gaɓar Kinidus. Da iskar ta hana mu ci gaba, sai muka bi ta bayan tsibirin Kirit ɗaura da Salmone.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُكَيِ ݣُونَ دَ ݣُونَكِے مُنَ تَڢِيَ أَ حَنْكَلِ، حَرْ دَݣَرْ مُكَ كَيْ كُسَدَ غَرِنْ كِنِدُسْ؞ دَ إِسْكَ تَحَنَ مُثِيغَبَ، سَيْ مُكَ ذَاغَيَ غٜىٰڢٜىٰنْ دَ بَ إِسْكَ، وَتُواْ تَبَايَنْ ڟِبِرِنْ كِرِتْ كُسَدَ سَلْمُواْنِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Muka yi kwana da kwanaki muna tafiya kaɗan kaɗan, har da ƙyar muka kai kusa da Kinidas. Da dai iska ta hana mu ci gaba, muka zaga ta bayan tsibirin Karita kusa da Salmoni.