Acts 28:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
’Yan’uwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ مَاسُبِے نَ رُواْمَ سُكَجِ لَابَرِنْمُ، سَيْ سُكَذُواْ سُمَرَبْثٜىٰمُ حَرْ أَ كَاسُوَرْ أَڢِّيُسْ دَ كُمَ وُرِنَّنْ دَ عَكٜىٰثٜىٰ دَشِ مَسَوْكِ عُكُ؞ دَ بُلُسْ يَغَنْسُ كُوَ يَيِ غُواْدِيَ غَ اللَّهْ ، يَكُمَ ڧَارَ سَامُنْ ڧَرْڢِنْ ڠُوِوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da 'yan'uwa na can suka ji labarinmu, sai da suka zo don su tarye mu har Kasuwar Abiyus, da kuma wurin nan da ake kira Maciya Uku. Da kuwa Bulus ya sadu da su, ya yi godiya ga Allah, jikinsa kuma ya yi ƙarfi.