Acts 28:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu, “’Yan’uwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da al’adun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ ݣُونَ عُكُ، بُلُسْ يَكِرَا مَنْيَنْ يَهُودَاوَا؞ دَسُكَ تَارُ سَيْيَثٜىٰمُسُ «كُو یَنْعُوَ، كُواْدَيَكٜىٰ بَنْيِ وَجَمَعَرْمُ وَنِ لَيْڢِے بَ، كُواْ لَيْڢِے غَمٜىٰدَ أَلْعَادُنْ كَاكَنِّنْمُ، دُكْدَهَكَ أَنْكَامَنِ أَ عُرُوشَلِيمَ عَكَ بَادَنِ غَ رُواْمَاوَا أَطَوْرٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan kwana uku ya kira manyan Yahudawan birnin. Da suka taru sai ya ce musu, “Ya ku 'yan'uwa, ko da yake ban yi wa jama'armu wani laifi ba, ko laifi a game da al'adun kakanninmu, duk da haka an bashe ni ɗaurarre ga Romawa tun daga Urushalima.