Acts 4:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تُواْ دَ شُوغَبَنِّنْ سُكَغَ ڧَرْڢِنْ حَلِنْ بِتْرُسْ دَ يَحْيَى، سُكَ كُمَ غَانٜىٰ سُمَرَسَ عِلِمِ نٜىٰ، تَلَكَاوَا كُمَ، سَيْ سُكَيِ مَامَاكِ، سُكَ كُوَ غَانٜىٰ ثٜىٰوَ دَا مَنْذَنِّےنْ سُنَ تَرٜىٰدَ عِيسَىٰ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yahaya, suka kuma gane marasa ilimi ne, talakawa kuma, suka yi mamaki, suka kuwa shaida su, a kan dā suna tare da Yesu.