Acts 5:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Nan take ta fāɗi a ƙafafunsa ta mutu. Sai samarin suka shigo ciki, suka kuwa same ta matacciya, suka ɗauke ta suka kai ta waje suka binne ta kusa da mijinta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نَنْ تَكٜىٰ تَڢَاطِ أَغَبَنْسَ، تَمُتُ؞ دَ سَمَارِنْ سُكَ شِغُواْ سُكَ سَامٜىٰتَ تَمُتُ، سَيْ سُكَ طَوْكٜىٰتَ، سُكَ ڢِتَرْدَ عِتَ، سُكَ بِنّٜىٰتَ تَغٜىٰڢٜىٰنْ مِجِنْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Nan tāke, ta fāɗi a gabansa, ta mutu. Da dai samarin suka shigo, suka iske ta matacciya, suka ɗauke ta suka fitar da ita, suka binne ta a jikin mijinta.