Acts 5:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane. Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَسُكَجِ حَكَ، سُكَ شِغَ هَيْكَلِنْ دَ سَسَّڢٜىٰ، سُنَ كُواْيَرْوَا؞ سَعَدَّ بَبَّنْ ڢِرِسْتِ دَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ تَرٜىٰ دَشِ سُكَ تَارُ، سُكَ كِرَا مَجَلِسَ دَ دُكَنْ شُوغَبَنِّنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، سُكَ عَيْكَ ذُوَا كُرْكُكُ عَكَٰوُاْ مَنْذَنِّےنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da suka ji haka, suka shiga Haikalin da sassafe, suna koyarwa. To, babban firist ya fito, shi da waɗanda suke tare da shi, suka kira majalisa, da dukan shugabannin Isra'ilawa, suka aika kurkuku a kawo su.