Acts 6:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan a asirce suka zuga waɗansu mutane su ce, “Mun ji Istifanus ya faɗa kalmomin saɓo game da Musa da kuma Allah.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَ ذُغَ وَطَنْسُ مُتَنٜىٰ عَٻُواْيٜىٰ دُواْمِنْ سُثٜىٰ «مُنْجِيشِ يَنَ ذَاغِنْ أَنَّبِے مُوسَٰى، يَنَيِ وَ اللَّهْ مَغَنَرْ رٜىٰنِ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka zuga mutane a asirce, su kuwa suka ce, “Mun ji shi yana zagin Musa, yana saɓon Allah.”