Acts 7:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kashegari, Musa ya sadu da Isra’ilawa biyu suna faɗa. Ya yi ƙoƙari ya sasanta su, yana cewa, ‘Ku mutane, ku ’yan’uwa ne, don me kuke so ku cutar da juna?’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَشٜىٰغَرِ كُمَ يَغَ وَطَنْسُ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا سُنَ ڢَطَ، سَيْ يَسُواْ يَشِرْيَسُ، يَثٜىٰ، ‹كُو جَمَعَ، كُو یَنْعُوَ نٜىٰ ڢَا، دُوانْمٜىٰ كُكٜىٰ ثُوتَرْ جُونَ؟›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kashegari kuma waɗansu suna faɗa, sai ya nemi shirya su, ya ce, ‘Ku jama'a, ku 'yan'uwa ne fa, don me kuke cutar juna?’