Acts 7:42 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Amma Allah ya juya musu baya ya kuma ba da su ga bautar abubuwan da suke a sararin sama. Wannan ya yi daidai da abin da yake a rubuce a cikin littafin annabawa cewa, “ ‘Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arba’in cikin, hamada, ya gidan Isra’ila?
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَبُواْدَ حَكَ اللَّهْ يَجُويَ مُسُ بَايَ، يَمِيڧَسُ غَ بَوْتَرْ رَانَ دَ وَتَ دَ تَوْرَرِنْ سَمَ؞ وَنَّنْ يَيِ دَيْدَيْدَ أَبِنْ دَيَكٜىٰ أَرُبُوثٜىٰ أَ لِتَّڢِنْ أَنَّبَاوَا ثٜىٰوَ « ‹كُو جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ، نِنٜىٰ كُكَ يَنْكَ وَ دَبُّواْبِے، كُكَ مِيڧَا وَ هَدَايَ، حَرْ شٜىٰكَرَا أَرْبَعِنْ عَثِكِنْ دَاجِ؟
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Saboda haka Allah ya juya musu baya, ya sallame su ga bautar taurari, yadda yake a rubuce a littafin annabawa cewa, ‘Ya ku jama'ar Isra'ila, Ni ne kuka yanka wa dabbobi, kuka miƙa wa hadaya, Har shekara arba'in a cikin jeji?