Acts 7:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Allah ya yi magana da shi ta haka, ‘Shekara ɗari huɗu, zuriyarka za tă yi baƙunci a wata ƙasar da ba tasu ba, za su yi bauta su kuma sha wulaƙanci.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
اللَّهْ كُوَ يَڢَطَا ثٜىٰوَ ذُرِيَرْ إِبْرَٰهِيمْ ذَاسُيِ بَڧُنْثِ أَوَتَ ڧَسَا، مُتَنٜىٰنْ ڧَسَرْ كُوَ ذَاسُ مَيْدَسُو بَايِ، ذَاسُبَاسُ وَهَلَ حَرْ شٜىٰكَرَا طَرِے حُطُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Abin da Allah ya faɗa kuwa shi ne zuriyar Ibrahim za su yi baƙunci a wata ƙasa, mutanen ƙasar kuwa za su bautar da su, su kuma gwada musu tasku har shekara arbaminya.