Amos 2:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sun tattake kawunan matalauta kamar yadda suke taka laka suka kuma danne wa marasa galihu gaskiya. Uba da ɗa su na kwana da yarinya guda, suna kuma ɓata sunana mai tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُنْ كُمَ تَتَّاكَ تَلَكَاوَا كَمَرْ سُنَ تَاكَ ڧُورَرْ ڧَسَا، بَاسَ شَرِيعَرْ غَسْكِيَ غَ مَرَسَ ڧَرْڢِے؞ بَابَ دَ طَنْسَ سُنَ ݣُونَ دَ مَثٜىٰ غُدَا؞ تَهَكَ سُكٜىٰيِنْ بَنْظَ دَ سُونَنَ مَيْ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sun tattake marasa ƙarfi da kāsassu, Suna tunkuɗe matalauta su wuce. Tsofaffi da samari sukan tafi wurin karuwan Haikali. Ta haka suke ɓata sunana mai tsarki.