Amos 2:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suna kwanciya kurkusa da kowane bagade a kan tufafin da suka karɓe jingina. A gidajen allolinsu sukan sha ruwan inabin da suka karɓo daga wurin waɗanda suka ci wa tara.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَغَبَنْ كُواْوَنٜىٰ بَغَدٜىٰ، سُنَ ݣُونْثِيَ عَكَنْ رِيغُنَنْ دَ عَكَ بَادَسُو جِنْغِنَ؞ أَ غِدَانَ سُنَ شَنْ ضُوً إِنَبِنْ دَ سُكَ سَيَ دَ كُطِنْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰبِنْسُ بَاشِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A duk wuraren sujadarsu sukan kwanta A bisa tufafin da suka karɓe jingina. A cikin Haikalin Allahnsu, sukan sha ruwan inabi Da suka karɓo daga wurin waɗanda suke bi bashi.