Amos 4:10 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Na aiko muku annoba yadda na yi a Masar. Na karkashe samarinku da takobi, tare da kamammun dawakanku. Na cika hancinku da warin sansaninku, duk da haka ba ku juyo gare ni ba” in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«نَا عَيْكَ دَ بَلَعِ عَثِكِنْكُ كَمَرْ يَدَّ نَيِ أَ مَصَرْ؞ نَا كَكَّشٜىٰ سَمَارِنْكُ دَ تَكُواْبِنْ يَاڧِ، نَا ݣُوشِ دَوَكِنْكُ؞ نَا ثِكَ حَنْثِنْكُ دَ وَرِنْ غَوَوَّكِنْ مُتَنٜىٰنْكُ دَ سُكَ مُتُ؞ دُكْدَهَكَ، بَكُ جُويَا وُرِينَبَ؞ نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Na aukar muku da annoba irin wadda na aukar wa Masar. Na karkashe samarinku a wurin yaƙi, Na kwashe dawakanku. Na cika hancinku da ɗoyin sansaninku. Duk da haka ba ku komo wurina ba.