Amos 4:6 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Na bar ku da yunwa a kowace birni, da kuma rashin abinci a kowane gari, duk da haka ba ku juyo gare ni ba,” in ji Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«نَسَا عَيِ يُنْوَ عَكُواْوَنٜىٰ بِرْنِنْكُ، دَ رَشِنْ عَبِنْثِ عَكُواْوَنٜىٰ غَرِ، دُكْدَهَكَ بَكُ جُويُواْ وُرِينَ بَ! نِے يَهْوٜىٰهْ نَا ڢَطَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce, “Ai, ni ne, na sa a yi yunwa a biranenku. Shi ya sa ba ku da abinci. Duk da haka ba ku juyo gare ni ba.