Amos 5:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta; ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a. Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin raguwar Yusuf.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُڧِ مُغُنْتَا، كُسُواْ أَبُ مَيْݣَوْ، كُكَڢَ شَرِيعَرْ غَسْكِيَ أَوُرِنْ تَارُوَ عَڧُواْڢَرْ غَرِ؞ وَتَڧِيلَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ مَيْ ضُنْدُنَا ذَيْ يِوَ ضَغُواْوَرْ ذُرِيَرْ يُوسُڢَ أَلْحٜىٰرِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta, Ku yi adalci cikin majalisar alƙalanku! Watakila Ubangiji Allah Mai Runduna Zai yi wa sauran da suka ragu na wannan al'umma alheri.