Amos 5:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi, ba zan karɓa ba. Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta, ba zan ɗauke su a bakin kome ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْ دَ كُنْ مِيڧَ مِنِ هَدَايُنْكُ نَڧُواْنَاوَا، دَ هَدَايُنْكُ نَهَڟِ، بَذَنْ كَرْٻَبَ؞ بَذَنْ كُمَ كَرْٻِ دَبُّواْبِنْكُ مَاسُ ڧِبَ وَطَنْدَ كُكَ مِيڧَ مِنِ هَدَايُنْ ڠَرَنْ زُمُنْثِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da kuka kawo mini hadayun ƙonawa Da hadayunku na tsaba, ba zan karɓa ba. Ba kuma zan karɓi turkakkun dabbobinku Waɗanda kuka miƙa mini hadayun godiya ba.