Amos 6:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ وَنِ دَغَ دَنْغِنْ وَنْدَ يَمُتُ، يَشِغَ غِدَنْ دُواْمِنْ يَڢِتَرْدَ غَاوَرْ يَڧُواْنٜىٰ، سَيْ يَيِ تَمْبَيَ كُواْ أَݣَويْ وَنِ عَٻُواْيٜىٰ ثِكِنْ غِدَنْ، يَثٜىٰ «كُواْ أَݣَويْ سَوْرَنْ غَوَوَّكِ؟» عِدَنْ أَنْ أَمْسَ «بَابُ،» مَيْ تَمْبَيَرْ ذَيْثٜىٰ «كُلْ، كَدَ كَعَمْبَثِ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ دُواْمِنْ كَدَ وَنِ أَبُ يَڢَرُ دَمُو؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?” Sai a amsa, “A'a.” Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.”