Amos 6:4 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa kuna mimmiƙe a kan kujerunku. Kuna cin naman ƙibabbun raguna da na ƙosassun ’yan maruƙa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَيْتُوانْكُ، كُو دَ كُكٜىٰ ݣُونْثِيَ عَكَنْ غَدَجٜىٰنْ دَ عَكَيِ دَ هَڧُواْرِنْ غِيوَ، كُنَ جِنْ دَاطِنْ مِيڧٜىٰ جِكُنَنْكُ أَ مَنْيَنْ كُجٜىٰرُنْكُ؞ كُنَ تَثِنْ نَامَنْ تُمَكِ دَغَ غَرْكٜىٰنْكُ دَ یَنْ شَانُو دَغَ طَكُنَنْ كِيوُانْكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Taku ta ƙare, ku da kuke kwance kan gadajen hauren giwa, Kuna jin daɗin miƙe jiki a dogayen kujerunku, Ku ci naman maraƙi da na rago.