Amos 7:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Ubangiji ya ɗauke ni daga kiwon dabbobi ya ce mini, ‘Je ka, ka yi wa mutanena Isra’ila annabci.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَهْوٜىٰهْ يَطَوْكٜىٰنِ دَغَ كِيوُانْ غَرْكٜىٰنْ تُمَكِ؞ يَثٜىٰ مِنِ، ‹تَڢِے، كَيِ أَنَّبْثِ غَ مُتَنٜىٰنَ نَ إِسْرَٰٓءِيلَ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Ubangiji ya raba ni da aikina na kiwo, ya umarce ni in tafi in yi magana da jama'arsa, wato Isra'ila.