Amos 7:17 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce, “ ‘Matarka za tă zama karuwa a cikin birni, kuma da takobi za a kashe ’ya’yanka maza da mata. Za a auna ƙasarka a kuma raba ta, kai kuma za ka mutu a ƙasar arna. Ba shakka Isra’ila za su tafi zaman bauta, nesa da ainihin ƙasarsu.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ إِنْجِ يَهْوٜىٰهْ ، ‹مَاتَرْكَ ذَاتَ ذَمَ كَارُوَ عَبِرْنِ، یَیَنْكَ مَظَا دَ مَاتَا، ذَاعَ كَكَّشٜىٰسُ دَ تَكُواْبِے؞ ڢِيلِنْ غُواْنَرْكَ، ذَاعَ رَرَّبَشِ، كَيْ كَنْكَ ذَاكَ مُتُ عَڧَسَرْدَ تَڧَظَنْتُ؞ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ كُوَ، حَڧِيڧَ ذَاعَ ݣُوشٜىٰسُ دَغَ ڧَسَرْسُ ذُوَا بَوْتَا أَوَتَ ڧَسَا؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
to, ga abin da Ubangiji ya ce maka, ya kai Amaziya, ‘Matarka za ta zama karuwa a birni, za a karkashe 'ya'yanka a cikin yaƙi. Za a rarraba wa waɗansu ƙasarka, kai kanka kuwa za ka mutu a ƙasar arna. Za a sa jama'ar Isra'ila su yi ƙaura zuwa wata ƙasa.’ ”