Amos 8:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ranakun suna zuwa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar, ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba, sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
إِنْجِ عُبَنْ‌غِجِ يَهْوٜىٰهْ ، «حَڧِيڧَ ݣُونَكِنْ سُنَ ذُوَا دَ ذَنْ عَيْكُواْ دَ يُنْوَ عَڧَسَرْ؞ بَ يُنْوَرْ عَبِنْثِبَ، بَ نَڧِشِنْ ضُوَبَ، عَمَّا يُنْوَرْ رَشِنْ سَامُنْ سَڧُوانْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Lokaci yana zuwa da zan aiko da yunwa a ƙasar. Mutane za su ji yunwa, Ba ta abinci ba, Za su ji ƙishi, Ba na ruwa ba. Za su ji yunwar rashin samun saƙo daga wurin Ubangiji. Ni Ubangiji ne, na faɗa.