Amos 9:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ranaku suna zuwa, in ji Ubangiji, “sa’ad da mai huɗa zai sha gaban mai girbi mai shuki kuma yă bi bayan mai matsin inabi. Sabon ruwan inabi zai ɗiga daga duwatsu yă kuma kwararo daga tuddai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَهْوٜىٰهْ يَا ثٜىٰ، «ݣُونَكِے سُنَ ذُوَا عِنْدَ مَيْ نُواْمَ ذَيْبِے بَايَنْ مَيْ غِرْبِے نَنْ دَنَنْ؞ مَيْ مَڟٜىٰوَرْ یَیَنْ إِنَبِے كُمَ ذَيْبِے بَايَنْ مَيْ شُوكَ نَنْ دَنَنْ؞ تُدَّيْ كُوَ ذَاسُدِنْ‌غَ ظُبُواْوَ سَابُوانْ ضُوً إِنَبِے، ڧأَنَانً تُدَّيْ كُمَ ذَاسُ ظُبَرْدَ ضُوً إِنَبِے كُواْعِنَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa, Sa'ad da girbi zai bi bayan huda nan da nan, Matsewar ruwan inabi kuma Za ta bi bayan shuka nan da nan. Duwatsu za su zubo da ruwan inabi mai zaƙi, Tuddai kuma su gudano da shi.