Colossians 2:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ina so ku san irin famar da nake yi saboda ku da kuma waɗanda suke a Lawodiseya, da kuma saboda dukan waɗanda ba su taɓa ganina ido da ido ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَمَا إِنَ سُواْ كُسَنْ إِرِنْ ڢَامَرْ دَنَكٜىٰيِ دُواْمِنْكُ دَ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ لَوُدِكِيَ دَ كُمَ دُكَنْ وَطَنْدَ بَسُ تَٻَ غَنِينَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
To, ina so ku san irin yawan shan faman da nake yi dominku, da waɗanda suke a Lawudikiya, da kuma duk waɗanda ba su taɓa ganina ba.