Colossians 4:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yana zuwa tare da Onesimus, ƙaunatacce da kuma amintaccen mai bin nan, wanda yake ɗaya daga cikinku. Za su gaya muku dukan abin da yake faruwa a nan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا كُمَ عُواْنِسِمُسْ تَرٜىٰ دَشِ، طَنْعُوَنْمُ مَيْ أَمِنْثِ وَنْدَ مُكٜىٰ ڧَوْنَ، وَنْدَ شِے مَا طَنْ وَجٜىٰنْكُنٜىٰ؞ سُو بِيُنْ ذَاسُ ڢَطَا مُكُ دُكَنْ أَبِنْدَ يَكٜىٰ ڢَرُوَ أَنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ga kuma Unisimas a nan tare da shi, amintaccen ɗan'uwa ƙaunatacce, wanda shi ma a cikinku yake. Su za su gaya muku duk abin da ya faru a nan.