Daniel 10:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai ya ce, “Daniyel, kai ne wanda ake ƙauna sosai, ka yi lura da kyau game da kalmomin da zan yi maka magana a kansu, ka tashi yanzu, gama an aiko ni a gare ka.” Sa’ad da ya faɗa mini haka, sai na tashi a tsaye ina rawan jiki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَثٜىٰ مِنِ «يَا دَانِيٜىٰلْ، كَيْ مَيْ دَرَجَ نٜىٰ سُواْسَيْ وَنْدَ اللَّهْ يَكٜىٰسُواْ، كَلُورَ دَ مَغَنَرْ دَ ذَنْ ڢَطَا مَكَ؞ كَمِيڧٜىٰ ڟَيٜىٰ، غَمَا أَوُرِنْكَ عَكَ عَيْكُواْ نِے؞» سَعَدَّ يَكٜىٰ ثِكِنْ ڢَطِنْ وَنَّنْ مَغَنَ، سَيْ نَمِيڧٜىٰ ڟَيٜىٰ، إِنَ ضَوَرْ جِكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ce mini, “Ya Daniyel, mutumin da ake sonka ƙwarai, ka lura da maganar da zan faɗa maka. Ka miƙe tsaye, gama a wurinka aka aiko ni.” Sa'ad da ya faɗi wannan magana, sai na miƙe tsaye, ina rawar jiki.