Daniel 10:13 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma mai mulkin masarautar Farisa ya tsare ni har kwana ashirin da ɗaya. Sai da Mika’ilu, ɗaya daga cikin manya shugabanni, ya zo ya taimake ni, saboda an tsare ni a can tare da sarkin Farisa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا شُوغَبَنْ ڧَسَرْ ڢَٰشِيَ يَيِ غَابَادَنِے حَرْ ݣُونَ عَشِرِنْ دَ طَيَ؞ عَمَّا مَلاَىِٕكَ مِيكَآءِيلُ، طَيَ دَغَ ثِكِنْ مَنْيَنْ شُوغَبَنِّ، يَذُواْ يَتَيْمَكٜىٰنِ، سَبُواْدَ عَكَ رِڧٜىٰنِ أَوُرِنْ تَرٜىٰدَ سَرَاكُنَنْ ڢَٰشِيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shugaban ƙasar Farisa ya tare ni har kwana ashirin da ɗaya, amma Mika'ilu, ɗaya daga cikin shugabanni, ya zo ya taimake ni, ya tsaya wurin sarakunan Farisa.