Daniel 11:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai yunƙura yă zo da ƙarfin dukan masarautarsa zai kuma nemi haɗinkan sarkin Kudu. Zai kuma ba shi diyarsa yă aura don yă lalatar da mulkin, amma shirinsa ba zai yi nasara ba ko yă taimake shi ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَيْسَا كَيْ دُواْمِنْ يَذُواْ دَ دُكَنْ إِيكُوانْ مُلْكِنْسَ؞ دُواْمِنْ عَثِ نَصَرَا عَكَنْ مُلْكٍ كُدُ، ذَيْ يِ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ دَ سَرْكِنْ كُدُ، كُمَ ذَيْ تَبَّتَرْ دَ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ تَوُرِنْ بَادَ یَرْسَ ثِكِنْ عَوْرٜىٰ غَ سَرْكِنْ كُدُ؞ عَمَّا وَنَّنْ دَبَرَ بَذَاتَثِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Zai yunƙuro da dukan ƙarfin mulkinsa, zai zo ya gabatar da shawarar salama, ya aikata ta. Zai aurar masa da 'yarsa don ta lalatar da mulkin abokin gabansa, amma wannan dabara ba za ta ci ba.