Daniel 11:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Magājin wannan sarki zai zama wani mutumin banza wanda ma bai fito daga gidan sarauta ba. Zai taso ba zato ba tsammani, yă ƙwace sarautar ta hanyar zamba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ وَنَّنْ مَيْ كَمَنِّنْ طَنْ أَدَمْ يَثِيغَبَدَ مَغَنَ يَثٜىٰ «بَايَنْ وَنَّنْ كُمَ وَنِ مُوغُنْ سَرْكِے ذَيْ غَاجِ سَرْكِنْ أَرٜىٰوَ؞ سَرْكِنَّنْ كُوَ بَيْ ثَنْثَنْثِ يِنْ مُلْكِبَ؞ ذَيْتَاسُواْ بَا ظَتُواْ بَا ڟَمَّنِ، يَڨُوثٜىٰ مُلْكٍ تَهَنْيَرْ ثُوتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Wani kuma rainanne zai maye gurbin wancan, shi kuwa ba ɗan jinin sarauta ba ne. Zai taso ba zato ba tsammani, ya ƙwace sarautar ta hanyar zamba.