Daniel 11:25 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Tare da babbar rundunar mayaƙa zai yi ƙarfin hali yă far wa sarkin Kudu da yaƙi. Sarkin kudu zai haɗa babbar rundunar soja mai ƙarfi don yaƙin, amma ba zai iya karo da shi ba, domin za a shirya masa maƙarƙashiya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَرْكِنْ أَرٜىٰوَ ذَيْ يِڧَرْڢِنْ ذُوثِيَا يَتَتَّارَ بَبَّرْ ڧُنْغِيَرْ سُواْجُواْجِ دُواْمِنْ يَكَيْ وَ سَرْكِنْ كُدُ يَاڧِ؞ سَرْكِنْ كُدُ شِے مَا ذَيْ تَتَّارَ بَبَّرْ ڧُنْغِيَرْ سُواْجُواْجِ مَيْ ڧَرْڢِے سُواْسَيْ دُواْمِنْ يَاڧِ؞ عَمَّا سَرْكِنْ كُدُ بَذَيْ عِيَ ڟَيَاوَا بَ، غَمَا ذَاعَيِ مَسَ ڧُلّٜىٰ ڧُلّٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Zai iza kansa ya yi ƙarfin hali ya kai wa sarkin kudu yaƙi da babbar rundunar soja. Sarkin kudu zai haɗa babbar rundunar soja mai ƙarfi don yaƙin, amma ba zai iya karo da shi ba, domin za a shirya masa maƙarƙashiya.