Daniel 11:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Sarkin Arewa zai koma ƙasarsa da dukiya mai girma, amma zuciyarsa za tă yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai ɗauki mataki a kan wannan abu sa’an nan yă koma ƙasarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً سَرْكِنْ أَرٜىٰوَ ذَيْ كُواْمَ ڧَسَرْسَ دَ دُوكِيَ مَيْ طُمْبُنْ يَوَ؞ ذُوثِيَارْسَ ذَاتَ يِغَابَادَ جَمَعَ تَيَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ مَيْ ڟَرْكِے؞ ذَيْ يِ يَدَّ يَغَ دَامَ، سَعَنً يَكُواْمَ ڧَسَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sarkin arewa zai koma gida da dukiya mai ɗumbun yawa. Zuciyarsa za ta yi gāba da tsattsarkan alkawari. Zai yi yadda ya ga dama sa'an nan ya koma ƙasarsa.